An rantsar da sabon firaministan Australia | Labarai | DW | 18.09.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An rantsar da sabon firaministan Australia

A wannan Larabar ce sabon firaministan Australia da jam'iyyarsa ta lashe zaben da aka yi a kasar a farkon wannan watan da muke ciki ya kama aiki.

Australia's conservative leader and Prime Minister-elect Tony Abbott gestures as he talks to the Secretary of the Department of the Prime Minister and Cabinet Ian Watt (not pictured), in Sydney September 8, 2013. Abbott swept into office in national elections on September 7 as voters punished the outgoing Labor government for six years of turbulent rule and for failing to maximise the benefits of a now fading mining boom. REUTERS/Daniel Munoz (AUSTRALIA - Tags: ELECTIONS POLITICS)

Sabon firaministan Australia Tony Abbott

Lokacin da ya ke shan rantsuwar kama aiki, Tony Abbott dan shekaru 55 da haihuwa ya lashi takobin yin aiki tukuru don kyautata rayuwar al'ummar kasarsa.

Abbott har wa ya yau ya yi alkawarin kawo karshen dumbin harajin da gwamnatin da ya gata ta sanyawa kamfanonin da ke kan gaba wajen gurabata muhalli, sannan kuma ya ce zai bijiro da wata doka nan take kan masu neman mafakar siyasa a kasar wadda za ta kunshi karkata akalar jiragen ruwan masu neman mafakar da suka isa kasar zuwa kasar Indonesia.

Gabannin wannan rantsuwar kama aikin da sabon firaministan ya yi, ya girka majalisar ministocinsa mai mai mambobi sha tara sai da wannan yunkuri da ya yi ya ci karo da suka daga ciki da wajen jam'iyyarsa kasancewar majalisar ministocin ta kushi mace guda kacal ne.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Umaru Aliyu