An rantsar da Obama a sabon wa′adin mulki | Labarai | DW | 20.01.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An rantsar da Obama a sabon wa'adin mulki

A kowace ranar 20 ga watan Janairu, kamar yadda kundin tsarin mulkin Amirka ya yi tanadi, ana rantsar da shugaban kasa, to sai dai a wannan karon lamarin ya faɗo ranar hutu a kasar.

default

Barack Obama

A wannan Lahadi ne aka rantsar da shugaba Barack Hussain Obama na Amirka a wani sabon wa'adin milkinsa na biyu. Kodayake a bisa ga al'adar kasar ta Amirka,ida har matakin rantsarda shugaban kasa da ake yi a kowace ranar 20 ga watan Janairu ya zo daidai da ranar lahadi kamar a wannan karon ,to ana shugulgullan ne ba a hukumance ba har sai ranar aiki ta kama wato Litanin inda za a gudanar da bukukuwan a hukumance.
Duk da wannan tsarin dai, daruruwan jama'a ne suka taru a wani gefe na fadar ta White House domin karama shugaban kasar da zai ci gaba da jagorancin kasar a wani sabon wa'adin milkinsa. An dai ga Obaman ya fito tare da mai dakinsa Michel da kuma mataimakinsa Joe Baedin suna gaida jama'a kamun ya yi jawabinsa ga mutanen.
Yanzu haka dai sabon shugaban na jan aiki mai tattare da kalubale a gabansa a ciki da wajen kasar ta Amurka.

Mawallafi: Issoufou Mamane
Edita: Usman Shehu Usman