1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabuwar gwamnatin ra'ayin rikau a Israila

Abdullahi Tanko Bala
December 29, 2022

Watanni biyu bayan zaben majalisun dokokin Israila an rantsar da sabuwar gwamnatin ra'ayin rikau ta Benjamin Netanyahu

https://p.dw.com/p/4LYVX
Israel Jerusalem neue Netanjahu-Regierung im Knesset
Hoto: AMIR COHEN/AP/picture alliance

Netanyahu mai shekaru 73 a duniya wanda ya dawo karagar mulki a karo na shida ya ce zai yi aiki wajen karfafa dangantaka da kasashen larabawa domin hana Iran mallakar makamin kare dangi.

An kuma zabi Amir Ohana na jam'iyyar Likud ra'ayin rikau ta Netanyahu a matsayin shugaban majalisar dokoki.

Gwamnatin wadda a karon farko ta kunshi 'yan siyasa masu ra'ayin rikau tsantsa na son aiwatar da sauye sauye da suka hada da rage karfin tasiri na bangaren shari'a.

Manazarta dai na kallo matakin a matsayin yunkurin soke tuhumar da ake yiwa Netanyahu wanda ke fuskantar shari'ar cin hanci da rashawa.