1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An rantsar da shugaban riko a Tunisiya

Abdul-raheem Hassan
July 25, 2019

Kakakin majalisar dokokin kasar Tunisiya Mohamed Ennaceur, ya sha rantsuwar kama aiki a matsayin shugaban kasa na wucin gadi jim kadan bayan rasuwar shugaban kasar na farko Beji Caid Essebsi.

https://p.dw.com/p/3Mk7Y
Tunesien Parlament in Tunis
Hoto: picture-alliance/AA/A. Landoulsi

Mukaddashin shugaban kasar ya yi alkwarin mutunta dokokin kasar Tunisiya, inda yake cewa: "Na yi rantsuwa ga Allah madaukakin sarki zan kare 'yancin kasar Tunisiya, kuma zan yi biyayya ga kundin tsarin mulki. Zan kare martaba tare da kula da bukatun al'ummar Tunsiya."

Ennaceur zai jagoranci kasar na tsawon watanni uku kamin sabon zabe. A yau ne dai Shugaban kasar ta Tunisia Beji Caid Essebsi ya kwanta dama yana shekaru 92 bayan fama da jinya.

A ranar Asabar ne aka shirya jana'aizar tsohon shugaban, yayin da gwamnatin kasar ta ayyana zaman makoki na kwanaki bakwai. Shugabannin kasashen larabawa da na sassan duniya na ci gaba da aiko da sakonnin ta'aziyar mutuwar Shugaba Essebsi.