1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ibn Chambas ya nemi kawo karshen ta'addanci

Ramatu Garba Baba
January 9, 2020

Babban wakilin Majalisar Dinkin Duniya na yankin yammancin Afirka da kuma Sahel Mohamed Ibn Chambas, ya baiyana fargaba kan karuwar ayyukan ta'addanci a kasashen Burkina Faso da Mali da kuma Jamhuriyyar Nijar. 

https://p.dw.com/p/3VvGY
UN-Sicherheitsrat | Nahost-Sitzung
Hoto: picture-alliance/AP Photo/M. Altaffer

Mohamed Ibn Chambas ya fadi hakan ne a yayin da ya ke jawabi a gaban wani taro na kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya, ya kara da cewa, lokaci yayi da shugabanin kasashen da suka dauki alkawarin yakar ta'addanci su tashi tsaye su kuma hada karfi da karfe don ganin sun magance matsalar tsaron kamar yadda aka amince a can baya, ya dai ja hankulan shugabanin kasashen Afrika da cewa, sai sun dage muddun suna son ganin sun inganta yanayin rayuwar al'ummarsu.


Mutum fiye da dubu hudu ne suka mutu a sakamakon hare-haren mayakan jihadi a shekarar 2019 idan aka kwatanta da rayuka dari bakwai da saba'in da suka salwanta a shekarar 2016 inji jami'in.