An nemi Catherine Samba Panza da tayi Murabus | Labarai | DW | 07.10.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An nemi Catherine Samba Panza da tayi Murabus

Tun bayan kafa gwamnatin da aka kira ta hadin kan 'yan kasa a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, kawo yanzu ana fuskantar tabarbarewar lamurra a wannan kasa.

Bayan wani babban zaman taro da suka gudanar a birnin Bangui, babban jagoran kungiyar 'yan Anti-Balaka a wannan kasa Patrice Edouard Ngaissona, yayi kira ga wakillan su dake cikin gwamnati da su fuce daga gwamnatin, tare kuma da baiwa Shugabar kasar ta rikon kwarya Catherine Samba Panza wa'adin kanaki biyu na tayi murabus, amma ba tare da ya bayyana abun da zai biyo baya muddin bata bi umarnin nsu ba.

Shugaban na Anti-balaka dai na zargin shugabar kasar ta rikon kwarya da nuna gazawa, inda yace babu yarda tsakaninta da al'umma, sannan kuma ya ce ta nemi taimakon daga shugaban kasar Chadi, na ya bata dakaru da zasu yi tsaron lafiyar ta, abun da suke ganin cewa bai zai haifar da zaman lafiya a wannan kasa ba.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Umaru Aliyu