An nemi a daina nuna kyama ga masu Ebola | Labarai | DW | 27.10.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An nemi a daina nuna kyama ga masu Ebola

Jakadiyar Amirka da ke zauren Majalisar Dinkin Duniya Samantha Power ta ce lokaci ya yi da za a daina nuna kyama ga masu dauke da Ebola.

Ms. Power ta kuma ce Amirka da sauran kasashen Duniya za su yi bakin kokarinsu wajen ganin an kawar da yaduwar cutar wadda yanzu haka ta hallaka mutanen da suka kai kusan dubu biyar yayin da wasu kimanin dubu goma ke dauke da ita.

Jakadiyar dai na wadannan kalamai ne yayin ziyararta a Gini, inda nan gaba kuma za ta isa Liberiya da Saliyo inda nan ma cutar ta yi ta'adin gaske da nufin ganewa idonta halin da ake ciki don sanin irin karin matakan da za dauka.

A wani labarin makamancin wannan, jami'an kiwon lafiya a Amirka sun ce suna sanya idanu kan wani karamin yaro da ya isa kasar daga Gini a karshen makon wanda yanzu haka ya ke fama da zazzafan zazzabi da kuma amai, wanda dukanninsu alamu ne na kamuwa da Ebola. To sai dai jami'an kiwon lafiya sun ce ya zuwa yanzu ba su kai ga tantacewa ko ya na dauke da cutar ba.