1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An nada tsohon jagoran tawaye minista a Kwango

March 24, 2023

Shugabn kasar Kwango Felix Tshisekedi, ya bai wa magudun tawayen kasar Jean-Pierre Bemba matsayin ministan tsaro. Mr. Bemba dai tsohon mataimakin shugaban kasa ne.

https://p.dw.com/p/4P9vF
Jean-Pierre Bemba na Kwango
Jean-Pierre BembaHoto: Getty Images/AFP/F. Coffrini

A wani garambawul din da ya yi wa majalisar ministocinsa a wannan Juma'a, Shugaba Felix Tshisekedi na Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango, ya nada tsohon jagoran tawayen kasar Jean-Pierre Bemba a matsayin ministan tsaro.

Mr. Bemba wanda ya kasance tsohon mataimakin shugaban kasa tsakanin 2003 zuwa 2006 a Kwangon, kotun hukunta masu aikata laifuka ta duniya ta daure shi a baya saboda wasu laifuka da wasu 'yan tawaye suka aikata a karkashin jagorancinsa.

Daga bisani kotun ta duniya a shekarar 2018 ta sauya matsayinta kan hukuncin.

Yanzu dai Kwangon na fama da neman hanyoyin kawo karshen yaki tsakaninta da mayakan tawayen M23, yakin da gwamnatin kasar ke zargin makwabciyarta Ruwanda da taimaka wa 'yan tawayen.

Cikin watan Disambar wannan shekarar ce dai za a gudanar da zabe a Kwangon.