An nada Theresa May a matsayin firaministan Birtaniya | Labarai | DW | 13.07.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An nada Theresa May a matsayin firaministan Birtaniya

Firaministan Birtaniya David Cameron tare da rakiyar mai dakinsa da ya'yansa guda uku ya je a fadar sarauniya Eliszabeth inda ya mika takardasa ta marabus ga sarauniyar .

Firaministan ya yi jawabi jum kadan bayan ya yi marabus.
Yace : ''Ina yin alfari a duk tswon rayuwata da irin wannan karamci da na samu na bautawa kasata a matsayin firaminista a cikin shekaru shida kana na kasance jagoran jam'iyyata a tsawon shekaru 11.''

Theresa May 'yar shekaru kimani 59 ita ce sarauniyar ta nada a matsayin sabuwar shugabar gwamnatin wacce ta sha rantsuwar kama aiki bayan marabus din na David Cameron.