An nada sabon shugaba kasa a Yukraine | Labarai | DW | 23.02.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An nada sabon shugaba kasa a Yukraine

Majalisar dokokin kasar Yukraine ta zabi Oleksandr Turchynov a matsayin shugaban wucin gadi

Ukraine Krise Alexander Turtschinow 22.02.2014 2013

Sabon shugaban Yukraine, Oleksandr Turchynov

A wannan Lahadi (23/02/2014) majalisar dokokin kasar ta Yukraine ta kada kuri'ar zaben kakakinta, Oleksandr Turchynov a matsayin shugaban kasa, kwana guda bayan kada kuri'ar kawar da shugaba Viktor Yanukovych, bayan kwashe watanni ana zanga-zanga.

Sabon shugaban yana da alaka da tsohuwar Firaministar Yulia Tymoshenko, wadda aka sako daga gidan fursuna. Jim kadan bayan fitowar da daga gidan kaso,Tymoshenko ta yi wa dubban magoya bayanta da suka hallara a Kiev babban birnin kasar jawabi, a karon farko.

Ta gudanar da jawabin bayan shugaba Viktor Yanukovych ya fice daga birnin, sannan 'yan majalisa suka kada kuri'ar tsige shi, matakin da shugaban ya ce ya saba ka'ida. Amma kawo wannan lokaci, babu duriyarsa. Majalisar ta saka watan Mayu bana domin gudanar da zaben shugaban kasar ta Yukraine.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Usman Shehu Usman