1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matashi ya zama sabon ministan harkokin wajen Pakistan

Suleiman Babayo AS
April 27, 2022

Firaminista Shehbaz Sharif na kasar Pakistan ya nada Bilawal Bhutto-Zardari jigon jam'iyyar PPP kana matashi dan shekaru 33 a matsayin ministan harkokin wajen kasar.

https://p.dw.com/p/4AViM
Pakistan l  Bilawal Bhutto Zardari wurde zum Außenminister ernannt
Hoto: Anjum Naveed/AP/picture alliance

Firaminista Shehbaz Sharif na kasar Pakistan ya nada Bilawal Bhutto-Zardari a matsayin ministan harkokin wajen kasar, wanda yake zama da-ga tsohuwar Firamnista Marigayiya Benazir Bhutto wadda aka yi wa kisan gilla a karshen shekara ta 2007 lokacin gangamin yakin neman zabe.

Shi dai sabon ministan harkokin wajen Bilawal Bhutto-Zardari yana da shekaru 33 kuma jigo a jam'iyyar PPP, inda zai kasance cikin tawogar firamnistan yayin ziyarar neman zuba jari zuwa kasar Saudiyya.

Kawo yanzu sabon Firamnista Shehbaz Sharif na kasar ta Pakistan ya nada mambobin majalisar zartaswa 41, tun bayan da majalisar dokokin kasar ta kada kuri'ar yanke dauna ga tsohon Firaminista Imran Khan a farko wannan wata na Afrilu, kuma sabuwar gwamnatin tana da jan aikin farfado da tattalin arzikin kasar inda tashin farashin kayayyaki gami da faduwar darajar kudin kasar ke kara jefa dinbin jama'a cikin talauci.