An naɗa wani jami′in yan′ sanda da zai bincike Oscar Pistorius. | Labarai | DW | 21.02.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An naɗa wani jami'in yan' sanda da zai bincike Oscar Pistorius.

shugabar hukumar yan sanda a Afirka ta Kudu Riah Phiyega ta ce an naɗa wani sabon jagoran masu gabatar da ƙara domin ya maye gurbin Hilton Botha.

Hakan kuwa ya biyo bayan cewar dan sandar da ke gudanar da bincike akan lamarin, Botha shi kansa ana tuhumar sa da laifin yunƙuri aikata kisan kai a shekarun 2009. A lokacin da ya yi harbi akan wata motar ya na cikin neman wani mai laifi.

A gobe juma'a za a ci gaba da yin shari'ar ta ɗan wasan tsereren na Afirka ta Kudu, domin yanke hukunci a kan ba da belinsa. Wanda ake kyautata zaton cewar zai sami nasara.Ana dai tuhumar Oscar ne da laifin kashe buduwarsa a gidansa da ke Pretoria a makon jiya amma ɗan wasan ya musunta hakan.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Zainab Mohammed Abubakar