An naɗa sabon firaminista a Mali | Labarai | DW | 12.12.2012
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An naɗa sabon firaminista a Mali

Diango Cissoko shi ne ya maye gurbin Cheik Modibo Diarra , kuma ya ce abin da zai mayar da hankali a kai da farko shi ne sake ƙwato yankin arewacin ƙasar

Wani ƙudirin gwamnatin da gidan telbijan na ƙasar ta Mali ya baiyana wato ORTM ,ya sanar da cewar shugaban gwamnatin wucin gadi Dioncounda Traoré, ya naɗa Diango Cissoko a matsayin sabon firaministan.

Cissoko ɗan shekaru 62 da haifuwa shi ne ke riƙe da muƙamin mai sasantawa na ƙasar tun a cikin watan Mayo na shekara bara.

Da ya ke magana da manema labarai Diango Cissokon ya ce abu na farko da ke a gaban sa shi ne shirya zaɓe;da sake ƙwato yankin arewacin ƙasar daga cikin hanu yan'tawayen sannan kuma ya ce zai kafa gwamnatin haɗin kan ƙasa.Kuma ya ƙara da cewar.Ya ce ''tare gaba ɗaya cikin haɗin kai zamu iya fuskantar man'yan ƙalubalan da ke a gaban mu ga ƙasar da ta rabu gida biyu.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane

Edita : Halima Balaraba Abbas