An naɗa sabon fira minista a Chadi | Siyasa | DW | 22.11.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

An naɗa sabon fira minista a Chadi

Shugaba Idriss Deby ya naɗa Kalzeube Pahimi Deube wani masanin tattalin arziki a matsayin shugaban gwamnati.

Wannan mataki ya biyo bayan da fira ministan mai ci Djimrangar Danadji ya ajiye takardar marabus ɗin sa a jajibirin da 'yan majalisun dokokin na Chadi suka shirya kaɗa ƙuri'ar yanka ƙauna ga shugaban gwamnatin wanda aka naɗa a kan muƙamin a cikin watan Yuni da ya gabata.

Ana zargin tsohon shugaban gwamnatin da gaza samar da ci gaba

'Yan majalisun dokokin su 74 na jam'iyyar da ke yin mulki suna zargin tsohon shugaban gwamnatin mista Djimrangar da laifin rusa gwamnatin a karo da dama. Da kuma sa a cafke wasu 'yan majalisun ba kan ƙaida ba a sa'ilin da aka murƙushe wani yunƙurin kiffar da gwamnatin Idriss Deby a cikin watan Mayu da ya gabata. Ko da shi ke gwamatin ba ta fito hazza ba ta bayyana haka amma a lokacin da yake karanta sanarwa gwamnatin muƙadashin sakataran gwamnatin ya bayyana ƙudirin naɗa sabon fira ministan

Ya ce :'' A kan wannan ƙudiri na 11 sakin layi na uku gwamnatin ta naɗa Kalzeube Pahimi Deube a matsayin sabon firaminista ƙasar Chadi.''

Ra'ayoyin 'yan ƙasar a kan naɗin sabon fira ministan

Mista Kalzeube wanda shi ne fira minista na 16 sanane a fagen siyasar ƙasar wanda ya riƙe muƙamai na gwamnatin da dama,kuma ya fito ne daga yanki kudanci na ƙasar. Shin ko minene ra'ayin jama'a a kan naɗin.? ga dai irin bayyanin da wasu jama'ar suka yi. ''Muna ganin wannan zaɓi ya yi daidai fatan mu dai shi ne kada a sake rushe gwamnatin kwanaki kaɗan.'' Shi ko wannan cewa ya ke yi ''Ni abin da na ke fata shi ne wannan sabon fira minista ya yi aikin da ƙasar mu za ta ci gaba.''

Daga ƙasa za a iya sauraron wannan rahoto haɗe da hirar da Zainab Mohammed Abubakar ta yi da wakilinmu na Ndjamena.Abdourazak Garba Baba Ani

Mawallafi : Abdoulrazak Garba Baba Ani
Edita : Abdourahamane Hassane

Sauti da bidiyo akan labarin