An mai da Dzhokhar Tsarnaev gidan yari | Labarai | DW | 26.04.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An mai da Dzhokhar Tsarnaev gidan yari

Jami'an 'yan sanda a Amurka sun sanar da sake komar da mutumin da ake zargi da kai hari a lokacin gudun ya da kanin wani a Boston gidan yari.

'Yan sanda a Amurka sun ce an maida mutumin nan da ake zargi da kai tagwayen hare-haren nan Boston zuwa wajen da ake tsare da masu laifi a Fort Devens da ke Massachusetts domin ci gaba tsare shi da ma yi masa magani gabannin gurfanarsa gaban kuliya.

Kakakin 'yan sandan Drew Wade ne ya tabbatar da wannan labarin inda ya ce an kai Dzhokhar Tsarnaev dan shekaru sha tara da haihuwa gidan na yari ne a wannan Juma'ar bayan da ya shafe kwanaki a wani asibiti da ke birnin Boston inda nan ne ma aka yi wa wadanda harin ya rutsa da su magani.

A ranar litinin din da ta gabata ce dai aka chaji Tsarnaev laifin amfani da bama-bamai wajen hallaka mutane uku da kuma jikkata wasu da dama dab da lokacin da ake kammala gudun yada kanin wani a garin na Boston ranar sha biyar ga wannan watan da mu ke ciki.

Mawallafi : Ahmed Salisu
Edita : Zainab Mohammed Abubakar