An kwashe ma′aikatan diplomasiyan Amirka a Lahore | Labarai | DW | 09.08.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kwashe ma'aikatan diplomasiyan Amirka a Lahore

Amirka ta kwashe ma'aikatan ofishin jakadanci da ke birnin Lahore na kasar Pakistan.

Kasar Amirka ta kwashe daukacin ma'aikatan ofishin jakadancin kasar da ke birnin Lahore na kasar Pakistan, wadanda aiyukansu bai zama tilas ba, saboda gargadin da ta samu na yuwuwar kai hari.

Ma'aikatar harkokin wajen kasar ta ce, matakin ya biyo bayan barazana da ta samu wadda ke nuna yuwuwar kai harin. Sannan ma'aikatar ta gargadi Amirkawa kan su kaurace wa kasar ta Pakistan. Wannan ya zo dai dai lokacin da al'ummar kasar ta Pakistan wadanda galibi Musulmai ne, ke gudanar da bukukun Sallah bayan kammala Azumin watan Ramadan, wata mai tsarki ga al'umar Musulmai.

Saboda tsaron yuwuwar kai hari, kasar ta Amirka ta rufe ofisoshin jakadanci kimanin 20 a kasashen arewacin Afirka da Gabas ta Tsakiya.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Umaru Aliyu