1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kwantar da Hosni Mubarak asibiti

April 13, 2011

Duk da cewar Hosni Mubarak na kwance asibiti, wato kotu a Masar ta ƙaddamar da binciken sa kan zargin sama da faɗi da dukiyar ƙasa.

https://p.dw.com/p/10sYN
Hoto: picture-alliance/dpa

Wata kotu a ƙasar Masar ta bada umarnin cafke tsofan shugaban ƙasa Hosni Mubarak, bisa zargin rabda ciki da dukiyar ƙasa.Wannan umurni ya zo kwana ɗaya bayan da aka kwantar da tsofan shugaban a asibiti.

Dubunnan jam´a masu neman cenji su ka sake shirya zanga-zanga inda su ka buƙaci komitin soja da ke riƙwan ƙwarya a Masar ya bincike Mubarak da muƙƙarrabansa

Bayan zargin sama da faɗi, kotu na zarin Mubarak da aikata kisan gilla ga masu zanga-zangar neman cenji.

Wannan bincike da kotu ta ƙaddamar ya shafi Hosni Mubarak da ´ya´yansa guda biyu, Gamal da Alaa, da kuma wasu ministocin gwamnatinsa.

A wani bayani da ya yi a gidan talbajan na Alarabiya, Hosni Mubarack ya mussanta dukan zargin da ake yi masa, wanda ya dangata da makirci, domin zubda masa mutunci.

Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi

Edita: Zainab Mohamed Abubakar