1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kwantar da shugaban Katolika a asibiti

March 30, 2023

Rashin lafiyar shugaban Kiristocin na zuwa ne a yayin da ake tsaka da shirye-shiryen bukukuwan Ista, wanda a bisa al'ada limamin mabiya Katolikan kan jagoranci tarurruka dabam-dabam.

https://p.dw.com/p/4PTR6
Hoto: VINCENZO PINTO/AFP

An kwantar da shugaban Kiristocin Katolika na duniya Fafaroma Francis a wani asibiti da ke kasar Italiya. Fadar Vatican ta ce an kai shugaban asibiti ne a ranar Laraba biyo bayan wata cuta mai alaka da numfashi da ke damun sa.

Kamfanin dillancin labaran Faransa, AFP, ya ce tuni aka soke wasu daga cikin tarurrukan da aka tsara Fafaroman zai halarta a wannan Alhamis, ana kuma sa ran soke wasu daga cikin ganawar da aka tsara  zai yi da wasu jama'a a 'yan kwanaki masu zuwa, domin a cewar fadar Vatican, Fafaroman na bukatar hutawa a asibiti na wasu 'yan kwanaki.