An kori wasu manyan sojoji daga aiki a Cote d′Ivoire | Labarai | DW | 10.01.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kori wasu manyan sojoji daga aiki a Cote d'Ivoire

Shugaba Alassane Ouattara ya kori wasu mayan jami'an soji da na jandarma da kuma na 'yan sanda daga aiki bayan boran da sojoji suka yi a kasar.

Wani babban sakataran gwamatin shi ne ya sanar da korar jami'an ta gidan talabijan na kasar ba tare da ya ba da wani karin haske ba.Kwanaki biyu dai sojoin suka kwashe suna yin bore a garuruwan Bouake da Daloa da sauransu a game da kudadensu na albashi da suke ke bin gwamatin bashi kafin daga bisani gwamnatin ta sanssanta da su.