An kori ministan cikin gida na Kenya | Labarai | DW | 02.12.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kori ministan cikin gida na Kenya

Shugaban ƙasar Uhuru Kenyatta shi ne ya ba da sanarwar korar ministan bayan hare-haren da Ƙungiyar al-Shaabab ta kai a yanki arewa maso gabashin ƙasar.

Hukumomin ƙasar Kenya sun kori ministan cikin gida, kana kuma babban sefto janar na 'yan sanda ya jiye aikinsa,bayan harin da Ƙungiyar al-Shaabab ta kai a yankin arewa maso gabashin ƙasar kan iyaka da Somaliya wanda a ciki aƙalla mutane 36 suka mutu.

Masu aiko da rahotannin sun ce mayaƙan na kungiyar su kusan 20 suka kai hari a kusa da garin Mandera,inda suka buɗe wuta ga wasu mutanen masu aiki haƙo ma'adinai da ke yin barci da misalin ƙarfe 12 na dare Litini da ta gabata.