An kori mayakan IS daga wasu yankuna | Labarai | DW | 27.05.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kori mayakan IS daga wasu yankuna

Mayakan Kurdawa sun fatattaki tsagerun kungiyar IS daga wasu kauyuka na kasar Siriya

Mayakan Kurdawa suka samun nasarar fatattakar tsagerun kungiyar IS da ke ikirarin kafa daular Islama cikin wasu kauyukan mabiya addinin Kirista a yankin arewa maso gabashin kasar Siriya.

Hukumar kula da kare hakkin dan Adam ta kasar Siriya ta ce kimanin kauyuka 14 aka samu nasarar korar mayakan na kungiyar IS. A wani labarin dakarun kasar Iraki da taimakon mayakan sa-kai sun kewaye garin Ramadi, domin sake kwacewa daga hannun 'yan kungiyar ta IS. Wasu rahotanni sun nuna cewa ana fafatawa a wasu sassan birnin tsakanin bangarorin biyu.