An kori ma′aikatan haƙar ma′adanai 1500 a Afrika ta Kudu | Labarai | DW | 18.10.2012
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kori ma'aikatan haƙar ma'adanai 1500 a Afrika ta Kudu

Kamfanin haƙar ma'adanin Platinum na Gold Fields a Afrika ta Kudu ya bada sanarwar korar ma'aikatansa dubu da dari biyar saboda ƙin komawa bakin aiki da su ka yi.

Kamfanin na Gold Fields ya ce korar ma'aikatan ya zama wajibi soboda ƙin amsa kiran komawa aikin da su ka yi kamar yadda kakakin kamfanin Sven Lunche ya shaidawa manema labarai.

Mr. Lunche ya ƙara da cewar muddin sauran ma'aikatan da aka umarta su koma bakin aiki ba su koma ba zuwa gobe to fa kamfanin bai da wani zaɓi da ya wuce su ma ya sallame su daga aiki baki ɗaya.

Ma'aikatan kamfanin na Gold Fields dai sun bi sahun takwarorinsu da ke aikin haƙar ma'adanai a wasu kamfanonin ƙasar wajen tsunduma yajin aiki ne saboda sabani da ke akwai tsakaninsu da shugabannin kamfanin musamman ma dai game da batun albashi da kuma yanayin aiki.

Mawallafi : Ahmed Salisu
Edita : Mohammed Awal Balarabe