1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kira majalisar Lesotho

September 4, 2014

Firaministan Lesotho ya sake kira majalisar dokokin da aka dakatar kimanin watanni uku da suka gabata

https://p.dw.com/p/1D7Lw
Hoto: Imago/Xinhua

Firaministan kasar Lesotho Thomas Thabane ya bayyana shirin sake kiran majalisar dokokin kasar da aka dakatar tun watan Yuni, domin kawar zaman zullumin da ya janyo yuwuwar kifar da gwamnati, abin da yasa ya yi gudun hijira na tsawon kwanaki hudu zuwa kasar Afirka ta Kudu.

Firaministan ya fadi haka cikin jawabin da ya gabatar a wannan Alhamis, inda ya ce majalisar za ta koma bakin aiki ranar 19 ga wannan wata na Satumba, bayan amincewar Sarki Letsie III, yayin da mataimakin firaminista Mothejoa Metsing ya kawar da yuwuwar neman kada kuri'ar yanke kauna wa gwamnatin hadakar. Akwai yuwuwar bangarorin siyasar kasar ta Lesotho suna aiki da shirin sansantawa na kungiyar bunkasa tattalin arzikin kasashen kudancin Afirka.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Usman Shehu Usman