An kawo wani da ya kamu da cutar Ebola Jamus | Labarai | DW | 27.08.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kawo wani da ya kamu da cutar Ebola Jamus

Wannan shi ne karon farko da likitoci a Jamus za su yi wa wanda ya harbu da kwayoyin cutar Ebola jinya a cikin kasar.

An kwantar da wani ma'aikacin hukumar lafiya ta duniya WHO da ya harbu da kwayoyin cutar Ebola a asibitin jami'ar birnin Hamburg da ke arewacin Jamus. Kakakin hukumomin kiwon lafiya a Hamburg ya ce hukumar ta WHO ce ta bukaci da a kwantar da ma'aikacin nata a wannan asibiti, da ke zama daya daga cikin asibitocin kararru a Jamus, wanda kuma ke da cikakken tanadi kuma ya san yadda zai tinkari cutar mai saurin yaduwa. Wannan shi ne karon farko da za a yi wa wani da ya kamu da cutar Ebola jinya a Jamus. Alkalumman hukumar WHO sun nuna cewa ya zuwa yanzu ma'aikatan kiwon lafiya fiye da 240 suka harbu da kwayoyin cutar a kasashen Saliyo, Guinea, Liberiya da kuma Najeriya. Sannan 120 daga cikinsu sun rigamu gidan gaskiya.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Umaru Aliyu