An kawo karshen Yakin Nahr al-Bared | Siyasa | DW | 22.06.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

An kawo karshen Yakin Nahr al-Bared

Gwamnatin Lebanon ta sanar da murkushe mayakan sa kai na Fatah al-Islam da kuma kawo karshen yakin baki daya.

Sansanin yan gudun hijirar Palasdinawa a Nahr al-Bared

Sansanin yan gudun hijirar Palasdinawa a Nahr al-Bared

Ɗauki ba daɗin wanda aka shafe tsawon kwanaki 33 ana gwabzawa tsakanin sojojin gwamnatin ta Lebanon da yan ƙungiyar Fatah al-Islam, an kawo ƙarshen sa ne a yau ɗin nan bayan da gwamnatin Lebanon ta baiyana nasarar murƙushe yan takifen waɗanda ke da nasaba da ƙungiyar al-Qaída. Tarzomar ta Nahr al-Bared wadda ta yi sanadiyar mutuwar a ƙalla mutane 172, ita ce tarzoma mafi muni tun bayan yaƙin basasar ƙasar a tsakanin shekarun 1975 zuwa 1990.

Ministan tsaro na ƙasar ta Lebanon Elias al-Murr wanda ya baiyana nasarar gwamnati na murƙushe yan ƙungiyar Fatah al-Islam yace sojojin gwamnatin sun ƙwace dukkan yankunan da yan takifen suka ja daga, yana mai cewa za su cigaba da kai mus farmaki har sai ragowar yan takifen da suka saura sun miƙa wuya. Yace za kuma a cigaba da aikin tone nakiyoyin da yan takifen suka bine a ƙarƙashin ƙasa. Jim kaɗan bayan sanarwar nasarar da Ministan tsaron na Lebanon, Elias Murr ya bayar, yan ƙungiyar ta Fatah al-Islam waɗanda aka yi ƙiyasin basu wuce yan ɗaruruwa ba a wajen sansanin suka shaidawa Palasɗinawa masu shiga tsakani amincewar su ta dakatar da buɗe wuta. Murr yace an kashe yawancin shugabanin ƙungiyar ta Fatah al-Islam, yayin da ragowar mayaƙan suka sulale daga gaɓar sansanin na Nahr al-Bared suka kuma saje da jamaá fararen hula. Yace sojojin za su cigaba da yiwa sansanin ƙawanya har dukkan yan takifen tare da shugaban su Shaker al-Abassi sun miƙa kan su.

A halin da ake ciki yanzu a sansanin, ba shiga ba fita, sojojin sun hana hatta yan jarida kaiwa ga sansanin wanda a cewar Ministan tsaro Elias Murr zai cigaba da kasancewa ƙarƙashin kulawar jamián soji. Wata mace mai shekaru 35 da haihuwa wadda ta fake tare da dan ta a sansanin yan gudun hijira na Beddawi dake maƙwabtaka da Nahr al-Bared ta ce sun gwammace fita su zauna a rairayi, amma suna tsoron nakiyoyi da aka binne a ƙarƙashin ƙasa.

Daruruwan yayan Palasdinawan sun yi dandazo a wata makaranta ta majalisar ɗinkin duniya a sansanin na Beddawi suna cewa abin da suke buƙata shine komawa gidajen su a sansanin Nahr al-Bared amma ba tallafin abinci ba da ake basu. Fadan ya tattara ne a wajen sansanin inda yan takifen ke da rinjaye. Yarjejeniyar larabawa ta 1969 ta haramtawa Jamián tsaro shiga sansanoni goma sha biyu na yan gudun hijirar Palasɗinawa dake ƙasar Lebanon A kalla mutane 172 waɗanda suka haɗa da sojoji 76 da yan takife 60 da kuma fararen hula 36 suka rasa rayukan su a wannan faɗa.A ranar 20 ga Mayu aka fara tarzomar ta Nahr al-Bared bayan da Mayakan fatah al-Islam suka kai hari wata cibiyar sojin gwamnati.