An kawo karshen taron kare muhalli a Jamus | Siyasa | DW | 23.10.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

An kawo karshen taron kare muhalli a Jamus

An kammala taro na mako guda kan sauyin yanayi a nan birnin Bonn na tarayyar Jamus da nufin samun matsaya guda.

Taron yana da nufin nufin fida matsaya guda wadda shugabannin kasashen duniya za yi taro a kai a cikin watan gobe a binrin Paris na Faransa don amincewa da sabbon tsarin da za a yi amfani da shi wajen kawar da matsala ta sauyin yanayi.

Yayin taron dai an baje kolin tattauna batutuwa da dama inda aka tattauna kan gibin da ke akwai tsakanin kasashe masu tasowa da wannan matsala ta dumamar yanayi ta fi shafa da kuma kasashe masu hannu da shuni wadanda suke kan gaba wajen gurbata muhalli. Sai dai daga irin abubuwa da aka tattauna alamu na nuna cewar har yanzu akwai gibi babba tsakanin bangarorin biyu.

Mattais Söderberg da ke jagorantar guda daga cikin kungiyoyin masu zaman kansu da ke aiki a kasashe masu tasowa na daga cikin masu wannan ra'ayi inda yake cewar ci gaban da aka samu a zaman taro ba wani na azo a gani ba ne.

Wani lamari har wa yau kan wannan batu da ke ci gaba da jan hankali shi ne irin kudaden da za a fitar domin a tinkari wannan matsala, wanda kasashe da dama da ke fitar hayakin mai gurbata muhalli ya zuwa yanzu ba su kai ga iya bawa ba. Wannan ya sanya kasashe masu tasowa kira ga irin wadannan kasashe da lallai su cika alkawarunsu kana su tashi tsaye wajen rage yawan hayakin.

Abin jira a gani dai yanzu haka shi ne yadda za ta kaya da ma irin matsayar da za a cimma a babban taron da shugabannin duniya za su yi a cikin watan gobe a birnin Paris na Faransa.

Sauti da bidiyo akan labarin