An kawo karshen babban taron majami´ar Evangelika a Kolon | Labarai | DW | 10.06.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kawo karshen babban taron majami´ar Evangelika a Kolon

An kammala babban taro karo 31 na majami´ar Evangelika tare da yin wani kasaitaccen bukin addu´o´i a birnin Kolon. Mutane kimanin dubu 100 suka halarci bukin addu´o´in na yau. Shugaban taron Reinhard Höppner ya ce tarukan da aka kwashe kwanaki biyar ana yi a birnin na Kolon sun yi armashi, inda ya bayyana batun nan na tattaunawa tsakanin addinai dabam dabam da cewa ya kara samun karbuwa. A jawabin da yayi a yau Höppner ya yi kira da a nemi hanyoyin tattaunawa da ´yan ta´adda da kuma ´yan taliban a Afghanistan. Ya ce dukkan su ya kamata a gaiyace su zuwa kan teburin shawarwari. To amma ya ce za´a dauki lokaci mai tsawo ana tattaunawar kamar yadda ake yi a yankin GTT. Ya ce hakan ita ce hanyar samun zaman lafiya mai dorewa.