An kashe ′yan jarida biyu a Iraki | Labarai | DW | 07.07.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kashe 'yan jarida biyu a Iraki

'Yan ta'adda sun kashe wasu 'yan jarida guda biyu a wani kauyen da ke kudancin birnin Mosul da ke a arewacin Iraki.

'Yan jaridun biyu wadanda ke yi wa gidan talabijan na Huna Salaheddine aiki an kashe su ne a garin Iman Gharbi. Kuma kafar ta ce yanzu haka wani dan jaridar na uku shi ma ya makale a kauyen tare da gawar 'yan jaridar guda biyu sakamakon yadda 'yan tawayen na IS ke ci gaba da yin sintiri a kauyen.