1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kashe 'yan China a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya

March 19, 2023

A wannan Lahadin ne aka kai hari kan wata ma'aikatar da 'yan China ke a cikin sa inda rahotanni ke cewa an yi asarar rayukan baki sinawa. Gwamnati dai ta ce tana bincike.

https://p.dw.com/p/4OuWu
Hoto: Getty Images/AFP/I. Lieman

Wani hari da ake zargin na 'yan tawaye ne a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, ya yi ajalin wasu 'yan asalin kasar China tara wadanda ke aikin hakar ma'adinin gwal a kasar.

Sabon harin ya zo ne kwanaki kalilan bayan garkuwa da wasu 'yan China su uku a kusa da iyakar kasar da Jamhuriyar Kamaru.

Da safiyar Lahadin nan ne bayanai ke cewa maharan suka afka wa mahakar gwal din da ke a Chimbolo, inda suka bude wuta a kan masu gadi.

Ba da jimawa ba ne dai aka kaddamar da aikin hako ma'adinan a wannan waje.

Mahukunta a yankin sun ce suna nan suna bin sawun maharan, amma kuma ba su yarda da yin wani karin bayani ba.

Kafin yanzun dai ana zargin gwamnatin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiyar da gaza kare rayukan mazauna yankin musamman baki 'yan kasashen waje.