Mayakan Somaliya tare da goyon bayan dakarun Amurka sun kai somame kan wasu wurare biyu da mayakan al-Shabab ke tare motocin kasuwa su na kwacewa mutane kudi.
Jami'an kazalika sun shaidar da cewar, wasu hare haren da jiragen yakin Amurkan a daren jiya ya lalata wata motar bus da ke makare da wasu abubuwa masu fashewa mallakar tsagerun na al-Shabab. Sai dai babu bayani daga wajen dakarun na Amurka da ke fada a Afirka.
Mazauna Awdhegle, wani karamin garin manoma da ke gunduwar Shabellea kudancin Somaliyar, sun shaidarwa da kamfanin dillancin labaru na Associate Press cewar, sun ji karar amon wuta a daren jiyan da ma fashewar wasu abubuwa masu nasaba da bam.