An kashe wasu ′yan ƙasashen waje a Pakistan | Labarai | DW | 23.06.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kashe wasu 'yan ƙasashen waje a Pakistan

Wasu 'yan bindiga sun kashe wasu 'yan yawon shaƙatawa guda 11 'yan ƙasashen Yukren da China da kuma Rasha a wani yanki da ke a arewacin ƙasar .

Hukumomin tsaro sun ce mutanen sun buɗe wuta ne a kan baƙin da ke a wani Otel ɗin inda suke da masabki.

Gidan talabijan na ƙasar na Pakistan PTV ya ambato wani babban jami'in 'yan sanda Ali Sher na mai cewar a cikin waɗanda suka mutu a kwai 'yan ƙasashen Yukren guda biyar da ' yan China guda uku da ɗaya ɗan Rasha. Jami'in dai ya ƙara da cewar maharan sun kai harin ne a cikin dare lokacin da mutanen ke yin barci. Garin dai na Gligit-Baltisan da ke kan iyaka da China da Kuma Cachmire, ana ɗaukar shi a matsayin wani wuri mafi kwanciyar hankali a Pakistan.To sai dai a 'yan shekarun baya baya nan ya kasance wata cibiya da masu kishin addini ke kai hare-hare galibi a kan tsiraru 'yan Shi'a.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane

Edita : Umaru Aliyu