An kashe wasu jami′an tsaro na Nijar | Labarai | DW | 30.10.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kashe wasu jami'an tsaro na Nijar

Hukumomin tsaro na Nijar da Mali sun ce an kashe wasu jami'an tsaro na Nijar guda tara a yankin Tilaberi da ke yammancin ƙasar kan iyaka da Mali.

A cikin wata sanarwa ta haɗin gwiwa wadda ofisoshin ministocin tsaro na Mali da Nijar ɗin suka bayyana, sun ce wasu mayaƙan 'yan ta'adda da ke ɗauke da makamai sun kai wani rukuni na hare-hare a jere.

Wanda a ciki 'yan sanda biyar, da jandarma biyu suka mutu yayin da wasu ukku suka jikkata. 'Yan bindigar sun kai harin ne a kan wani sansanin 'yan gudun hijira na Mali na Mangaize da kuma gidan kurkuku na garin Walam.