An kashe wasu daliban kwalejin sojoji a Masar | Labarai | DW | 15.04.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kashe wasu daliban kwalejin sojoji a Masar

Ana yawaita kai hari kan dakarun tsaron Masar, hare-hare da kungiyoyi masu kaifi kishin addini ke daukar alhakinsu.

Dalibai biyu na wata kwalejin horas da sojojin Masare sun rasu sannan shida sun jikata a wani harin bam da aka kai kan wata karamar bas a birnin Kafr al-Sheikh da ke arewacin kasar. A kwanakin nan dai ana yawaita kai hari kan dakarun tsaron Masar, hare-hare da kungiyoyi masu kaifi kishin addini ke daukar alhakinsu. Sai dai wannan shi ne na farko da aka kai kan dalibai da ke da alaka da rundunar kasar. Masar dai na fama da hare-haren masu ta da kayar baya musamman a yankin Sinai inda aka kashe daruruwan da 'yan sanda tun bayan barkewar tashe-tashen hankula a tsakiyar shekara ta 2013 lokacin da hafsan sojojin kasar Abdel Fattah al-Sisi ya hambarar shugaban kasa Mohammed Mursi. Kawo yanzu ba wanda ya dauki alhakin kai harin na wannan Laraba.