An kashe wani sojin Majalisar Ɗinkin Duniya a Mali | Labarai | DW | 08.10.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kashe wani sojin Majalisar Ɗinkin Duniya a Mali

Rahotanni daga Mali na cewar wasu yan bindigar ne da ba a tantance ba,suka jefa gurneti a cikin rundunar dakarun kiyaye zaman ta MINUSMA da ke a Kidal na yankin arewacin ƙasar.

Wani kakakin rundunar ta MINUSMA Olivier Salgado wanda ya ce soji ɗaya ɗan asalin ƙasar Senagal ya mutu a ciki harin, ya ce 'yan bindigar sun jefa masu gurneti ɗai-ɗai har guda shida.

Hakan kuwa na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan kisan wasu dakarun rundunar ta MINUSMA su tara 'yan ƙasar Nijar. Wanda Ƙungiyar MUJAO ta masu kishin addini ta ɗauƙi alhaki, tuni dai Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi Allah wadai da harin.