An kashe wani na hannun damar shugaban Rasha | Labarai | DW | 07.11.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kashe wani na hannun damar shugaban Rasha

An gano gawar Mikhail Lesin miloniya kana tsohon ministan sadarwa na kasar ta Rasha a dakin Hotel The Dupont Circle na birnin Washigton.

Russland Moskau Mikhail Lesin Gazprom Medien Generaldirektor

Mikhail Lesin tsohon ministan sadarwar Rasha

An gano gawar wani tsohon ministan sadarwa na kasar Rasha na kusa da Shugaba Putin a dakin wani Hotel na birnin Washington babban birnin Amirka. Tashar talabijin ta ABC News ta kasar ta Amirka wacce ta ruwaito wannan labari da ta ce ta samu daga wasu manyan jami'an Rasha da Amirka, ta ce an gano gawar mutumin mai suna Mikhail Lesin wanda ya yi kaurin suna wajen tauye 'yancin aikin jarida a lokacin da yake rike da mukamin ministan sadarwar kasar ta Rasha a ranar Alhamis a wani daki na Hotel The Dupont Circle da ke a birnin na Washington

Tuni dai hukumomin kasashen biyu suka dukufa cikin binciken gano musabbabin mutuwar wanda yake daya daga cikin manyan attajiran kasar ta Rasha