An kashe wani mallami a Kenya | Labarai | DW | 05.11.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kashe wani mallami a Kenya

Hukumomin tsaro na ƙasar sun ce wasu 'yan bindigar waɗanda ba shaidasu ba sune suka harbe mallamin har lahira a birnin Mombasa.

Mallamin mai sunan Salim Bakari Muwarangi an harbeshi ne da bindiga a sa'ilin da ya fice daga wani masallaci da ke a kudancin ƙasar. Babban sefeto janar na 'yan sanda na Mombasa birnin na biyu mafi girma na ƙasar.

Ya ce mutane da suka harɓe mallamin sun zo ne kan babura kafin daga bisani su ware,kuma ya ce yanzu haka suna gudanar da bincike domin ganosu.A karo da dama ana kashe mallamai masu nuna adawa da Ƙungiyar al Shaabab a ƙasar ta Kenya