An kashe wani jami′in Al-Qaida a Iraƙi | Labarai | DW | 17.04.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kashe wani jami'in Al-Qaida a Iraƙi

Hukumomin Iraƙin sun ce an kashe Izzat Ibrahim al-Douri tsohon jami'in gwamnatin Saddam Hussein da ke da alaƙa da Al-Qaida.

Da yake magana da gidan Talabijin na al-Arabiya gwamna lardin Salahudin ya a ce ƙwararu masu yin gwajin ƙwayoyin halita na jini na ƙoƙarin tantance gawar domin haƙiƙance ko shi ne.

A karo da dama hukumomin Iraƙin sun sha ba da sanarwa mutuwar Al-Douri amma kuma a yanka ta tashi. Al-Douri dai wani jigo a cikin ƙungiyar masu tada ƙayar baya na IS, kuma ana ganin cewar ba ƙaramar nasara ba ce idan aka tabbatar da mutuwarsa.