An kashe tsohon shugaban kasar Yemen | Labarai | DW | 04.12.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kashe tsohon shugaban kasar Yemen

Rahotanni da ke fitowa daga Sanaa babban birnin kasar Yemen, na cewa kungiyar 'yan tawayen Houthi sun dauki alhakin kashe tsohon shugaban kasar Ali Abdallah Saleh mai shekaru 75.

Wani gidan rediyo a yankin 'yan tawayen Houthi ya fara wallafa labarin kashe tsohon shugaban kasar, amma babu wata majiya mai zaman kanta da ta tabbatar da labarin kawo yanzu.

Yankunan 'yan tawayen da ke iko da birnin Sanaa, ya fuskanci gwabza kazamin fada tsakanin sojojin gwamnati da ke samun goyon bayan sojojin Saudiyya, abin da ya zo bayan da tsohon shugaban kasar Yemen Ali Abdallah Saleh ya sanar da ballewa da kungiyar 'yan tawayen kasar da yake mara wa baya a shekarun da suka gabata.

Shugaban kasar Yemen na yanzu Abedrabbo Mansour Hadi ya umarci dakarun gwamnati da su gaggauta maida birnin Sanaa karkashin ikon gwamnati.