An kashe sojojin Chadi a Mali | Labarai | DW | 13.04.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kashe sojojin Chadi a Mali

Rahotanni daga Mali na cewar sojin kasar Chadi uku sun kwanta dama sakamakon wani harin kunar bakin wake da ya rutsa da su a birnin Kidal da ke arewacin kasar.

Da ya ke magana da kamfanin dillancin labarai na Reuters wani mazaunin garin Kidal inda aka kai harin ya ce wani dan kunar bakin wake ne ya tunkari wani gungu na sojin Chadi in bai yi wata-wata ba wajen tada bama-baman da ya ke dauke da su, wanda hakan ya yi sanadiyyar rasuwar sojin na Chadi uku nan take yayin da wasu dama su ka jikkata.

Tuni dai rundunar sojin ta Chadi da ke aiki a Mali din ta tabbatar da wannan labarin inda ta ce harin na jiya ya kawo yawan sojin su da su ka rasu a yakin na Mali ya zuwa talatin.

A wani labarin kuma, a jiya Juma'a ce ma'aikatar tsaron Mali ta ce wani jirgin yakinta mai saukar ungulu ya yi hadari a birnin Sevare da ke tsakiyar kasar wanda ya yi sanadiyyar rasuwar mutane biyar din da ke cikinsa nan take.

Kawo yanzu dai inji ma'aitakar tsaron kasar ba a tantance musababbin hadarin ba amma jami'an ta na nan su na gudanar da bincike domin gano musababbinsa.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Muhammad Awal Balarabe