An kashe sojoji bakoye a birnin Benghazi | Labarai | DW | 02.10.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kashe sojoji bakoye a birnin Benghazi

Wasu tagwayen hare-hare, da ma fadace-fadace da suka wakana a kewayan filin jirgin saman birnin Benghazi, sun hallaka sojoji tare da jikkata wasu da dama.

Hakan ta faru ne sakamakon wata fafatawa da akayi tsakanin sojojin gwamnatin kasar da kungiyoyin mayaka a cewa wata majiya ta sojan wannan kasa. Da farko dai wasu motoci ne shake da bama-baman ne suka tarwatse yayin da ayyarin wasu motocin soja ke ficewa a kusa da filin jirgin, inda nan take sojoji uku suka rasu, tare da jikkata wasu da dama, yayin da wasu sojojin guda hudu suka rasu a lokacin fafatawa a kewayan filin jirgin na Benghazi.

Tun dai farkon watan Satumba ne dai mayaka masu kishin Islama ke kokarin kwatar wannan filin jirgin wanda ya kumshi wani karamin filin jirgi na farar hulla, da kuma wata barakin soja, inda kusan kullu ake fafatawa tsakanin bengarorin.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Umaru Aliyu