An kashe mutumin da ya kitsa harin Paris | Labarai | DW | 19.11.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kashe mutumin da ya kitsa harin Paris

Hukumomin Faransa sun tabbatar da mutuwar Abdelhamid Abaaoud dan asalin kasar Belgiyam, da ake zargi da kitsa harin birnin Paris na ranar Jumma'ar da ta gabata.

Firaministan kasar ta Faransa Manul Valls ne ya tabbatar da wannan labari a gaban majalisar dokokin kasar lokacin mahawara kan batun tsawaita dokar ta baci da watanni uku a kasar.

Manuel Valls ya ce babban alkalin mai shigar da karana kasar ne ya tabbatar mashi da mutuwar Abdoulhamid Abaaoud daya daga cikin wadanda suka kitsa harin birnin Paris ya mutu a lokacin harin da 'yan sanda suka kay a jiya Laraba a Saint-Denis

Sai dai kuma yanzu haka hukumomin kasar ta Faransa sun saka ayar tambaya game da ingancin matakan leken asiri na kasashen Turai ganin irin yadda aka kasa samun wata kasa daya ta Turai da ke da bayanai kan Abdoulhamid Abaaoud din, wannan kuwa duk da irin shigi da ficin da ya ke gudanarwa iya son ransa a tsakanin kasashen nahiyar kafin mutuwar tasa.