An kashe mutane shida a jihar Filato | Labarai | DW | 08.05.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kashe mutane shida a jihar Filato

Rikicin ƙabilanci shi ne ya yi sanadiyyar ɓarkewar tashin hankalin tsakanin ƙabilun Irigwe da Rukuba a jihar ta Filato ta Najeriya.

Jami'an tsaro a jihar Filato na ƙoƙarin shawo kan tashin hankalin na ƙabilanci da ya ɓarke tsakanin ƙabilun Irigwe da Rukuba, cikin ƙaramar hukumar Bassa, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 6.

Ko da shi ke dai har ya zuwa wannan lokaci babu wani ƙarin bayyani dangane da sanadin tashin hankalin, to amma rahotannin sun ce an yi harbe-harbe a ƙauyen Dutsen Kura, tsakanin matasa 'yan ƙabilar Irigwe da Rukuba, inda mutane da dama daga ɓangarorin biyu suka sami raunuka. Wasu rahotannin sun ce an yi ƙone-ƙonen gidajen zama na jama'a, lamarin da ya sa wasu mazauna ƙauyen Kaltumai, da Dutsen Kura, suka ƙauracewa tashin hankalin zuwa neman mafaka a wasu ƙauyuka.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Umaru Aliyu