An kashe mutane 38 a jihar Kaduna-Najeriya | Labarai | DW | 24.06.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kashe mutane 38 a jihar Kaduna-Najeriya

Wasu 'yan bindiga da ke sanye da kakin soji waɗanda ba a shaida su ba, sun kai hari a Karshi da Nandu inda suka kashe mata da yara ƙanana.

Hukumomin yankin sun ce an kashe mutane 21 a ƙauyen Karshi yayin da wasu 17 suka hallaka a Nandu, sannan sun ƙara da cewar ba su da masaniya dangane da waɗanda suka kai hare-haren.

Wani kakakin gwamnan jihar ya tabbatar da harin, sai dai ya ƙi ya bayyana ko waɗanne ƙabilu ne lamarin ya shafa. Jihar ta Kaduna na ɗaya daga cikin jihohin Najeriya da ke fama da rikicin addini da na ƙabilanci. A cikin watan Maris da ya gabata sama da mutane guda ɗari suka mutu a wani faɗan da aka gwabza na rikicin addini.

Mawallafi: Abdourahamane Hassane
Edita : Mouhamadou Awal Balarabe