An kashe mutane 19 a wani hari kan gidan adana kayan tarihi a Tunisiya | Labarai | DW | 18.03.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kashe mutane 19 a wani hari kan gidan adana kayan tarihi a Tunisiya

Wasu 'yan bindiga biyu da ake zargi mayakan kungiyar IS ne sukam kai harin kan gidan tarihin na Bardo.

Wasu 'yan bindiga a cikin kayan soji sun farma gidan ajiye kayan tarihi a kasar Tunisiya inda suka kashe baki 'yan yawon bude ido 17 da 'yan kasar ta Tunisiya biyu, a wani harin 'yan bindiga da ke zama daya daga cikin mafiya muni a kasar. Baki daga kasashen Italiya da Jamus da Poland da kuma Spaniya na daga cikin wadanda suka mutu a harin da aka kai kan gidan ajiye kayan tarihi na Bardo da ke kusa da majalisar dokoki da ke Tunis babban birnin kasar ta Tunisiya. Dakarun tsaro sun kai dauki sa'o'i biyu bayan harin inda suka kashe maharan su biyu sannan suka kubutar da sauran wadanda aka yi garkuwa da su a cikin ginin. An kashe dan sanda daya. Babbar jami'ar da ke kula da harkokin ketare na tarayyar Turai Federica Mogherini ta ce mayakan IS da ke ta da kayar baya a Libiya su suka kai harin.