1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kashe jami'an sa kai a Kenya

May 12, 2021

Jami'an 'yan sanda sa kai uku ne wasu 'yan bindiga suka kashe a kusa da iyakar Kenya da Somaliya a wani yunkuri na datse kafofin sadarwar kasar.  

https://p.dw.com/p/3tJul
Kenia Nairobi Coronavirus Ausgangssperre Patrouille Kontrolle
Hoto: picture-alliance/AP Photo/B. Inganga

Mayakan Al-Qaeda da na Al-Shabaab dai sun kai hari ne ga babbar layin waya da ke gudummar Mandera yayinda suka yi yunkurin kai wani harin a gundummar Wajir.

Kungiyar Al-Shabab dai ta sha alwashin daukar fansa kan Kenya saboda tura wa da dakarunta Somaliya don yakar masu tada kayar baya. Dakarun na Kenya dai suna yaki tukuru a Somaliya tun daga shekarar 2011, lokacin da aka tura su biyo bayan garkuwa da Turawa na ta'azarra a kasar wanda aka daura alhakin hakan ga mayakan.