1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Habasha: An halaka jagoran aikin gina babban dam na Afirka

Gazali Abdou Tasawa
July 26, 2018

Rahotanni daga kasar Habasha na cewa an bindige har lahira daraktan da ke kula da aikin gina babbar madatsa ruwan da za ta wadatar da kasar da makamashi.

https://p.dw.com/p/329Bc
Äthiopien, Simegnew Bekele, Projektleiter des Grand Ethiopian Renaissance Dam (GERD)
Hoto: DW/T.Waldyes

 Hukumar 'yan sanda ta birnin Adis Ababa ta ce an kashe injiniyan mai suna Simegnew Bekele da bindiga da rana tsaka a dandalin Meskel na tsakiyar birnin Adis Ababa. 

Kawo yanzu dai ba a kai ga gano ko su wa ne suka aikata wannan kisa ba, kuma a bisa wani dalili aka aikata shi. Wannan dam da kasar Habasha ke ginawa kusa da kan iyakarta da Sudan shi ne dam mafi girma a nahiyar Afirka wanda zai samar da megawatt dubu shida wato kwatankwacin karfin tashoshin makamashin nukiliya guda shida. 

Dama dai wannan aiki wanda aka soma tun a shekara ta 2011 na shan suka daga kasar Masar wacce ke fargabar cewa gina wannan dam a saman kogin Nil zai rage yawan ruwan kogin a cikin kasarta, alhali kogin ne ke samar da kaso 90 daga cikin dari na bukatar ruwan yankin. Mahukuntan kasar ta Habasha dai sun sanar da soma gudanar da bincike kan lamarin.