An kashe jagoran addini a Bangladesh | Labarai | DW | 11.04.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kashe jagoran addini a Bangladesh

An rataye Muhammad Kamuruzama a gidan kurku byan kotu ta sameshi da laifi kisan ƙare dangui.

Muhhamad dan shekaru 63 jagoran jam'iyyar 'yan adawa ta masu kishin addini,wata kotun ta musammun da aka girka ta sameshi da hannu a kisan ƙare dangi da aka aiwatar a lokacin yaƙin samun yanci kai na ƙasar daga Pakistan a shekarun 1971.

Tun da farko kotun ƙollin ƙasar ta yi watsi da ƙaran da ya ɗaukaka a kan hukuncin kisan.