1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Harin kan fararen hula a Burkina Faso

Abdourahamane Hassane
May 19, 2023

An kashe fararen hula guda 20 da suka hada da mata da kananan yara a yayin wasu hare-hare biyu da ake zargin mayakan jihadi suka kai a tsakiyar gabashin Burkina Faso a cewar majiyoyin tsaro.

https://p.dw.com/p/4Rb0a
Burkina Faso Trauer Tote Anschlag
Hoto: Vincent Bado/REUTERS

Kungiyoyi masu dauke da makamai sun kai farmaki cikin garin Bilguimdure, wani kauye da ke cikin gundumar Sangha, a lardin Kulpélogo da ke a tsakiyya maso gabashin Burkina Fason mai iyaka da kasashen Ghana da Togo, inda suka kashe mutane goma. Kasar Burkina Faso, wacce ta fuskanci juyin mulki har sau biyu a shekarar ta 2022, ta fada cikin tashin hankali na masu jihadi a shekara ta 2015. wanda ya yi sanadin mutuwar mutane fararen hula da sojoji fiye da dubu goma.