1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kashe masu taimaka wa sojoji a Burkina Faso

Abdourahamane Hassane
May 16, 2022

Kimanin masu taimaka wa sojoji a aikin tabbatar da tsaro 40 ne hade da farar hula aka kashe a wasu hare-hare da aka kai a arewa maso gabashin Burkina Faso.

https://p.dw.com/p/4BN5d
Symbolbild I Sicherheitsbeamte Burkina Faso
Hoto: Ahmed Ouoba/AFP/Getty Images

Harin ya rutsa da 'yan kato da gora da wasu fararan hular a gundumar Guessel da ke a yankin arewaci. Bayan da aka samu saukin hare-hare a tsawon makwanni, a halin yanzu gwamnatin mulkin sojan ta Damiba na fuskantar karuwar hare-haren wanda aka kiesta cewar a kasa da makwanni uku mayakan jihadi  sun kashe fararen hula da sojoji sama da dari.