An kashe dan sanda a majalisar dokokin Amirka | Labarai | DW | 03.04.2021
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kashe dan sanda a majalisar dokokin Amirka

Wani mahari ne ya kutsa kai a harabar majalisar dokokin da mota, sannan ya zaro wuka ya bi kan jami'an tsaron da ke gadin majalisar a birnin Washington.

Rahotanni sun ce sauran 'yan sandan da suka tsira dakyar, sun bindige maharin mai shekaru 25 nan take, sai dai haryanzu ba a tabbatar da ko harin yana da alaka da harin ta'addanci ba.

Shugaban Amirka Joe Biden ya yi tir da sabon harin, tare da aika sakon jaje ga iyalan dan sandan da ya rasa ransa. Harin ya faru ne watanni uku bayan kai makamancinsa a Capitol, inda ake zargin 'yan jagaliyar siyasa magoya banan tsohon Shugaban kasar Donald Trump ne suka kai harin kan takkadamar zaben 2020.